Kungiyar Kwararrun Injiniyoyi Ta Kasa karkashin jagorancin Takumbo Ajaye, ta bayyana aikin ginin fadar masarautar Kano yake da inganci tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka.
Shugaban kungiyar Injiniya Takumbo Ajayi ne bayyana haka a yayin ziyarar ban girma ga sarkin Kano Muhammadu Sunusi shi da tawagarsa a fadar kano a ranar Alhamis.
”Inganci ginin masarautar Kano na nuna cigaba wajen fito da ingancin al’adu da kuma bada sha’awa ga masu yawon bude ido.” In ji shi.
A jawabin Mai martaba sarkin kano Muhammadu Sunusi na II ya godewa shugabannin kungiyar bisa nuna kishinsu da fito da tsarin gine ginen al’adunmu na gargajiya.
