Hukumar zabe mai zaman kan ta kasa INEC ta sanar da lokucin gudanar da zabukan cike gurbi a mazabu 16 dake jihohi 12 na kasa.
Shugaban hukumar Farfesa Muhamud Yakubu ya sanar da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsai na hukumar da jam’iyyun siyasa a ALhamis din nan.
Farfesa Yakubu yace hukmar ta ware ranar 16 ga watan Agustan 2025 domin gudanar da zabukan.
Yace za a gudanar da zabukan cike gurbin ne a mazabar Bagwai da Shanono dake nan Kano.
Idan za a iya tunawa dan majalisar tarayya mai wakiltar Bagwai da Shonono Halilu Ibrahim Kundila na jam’iyyar APC ya rasu a ranar 6 ga watan AFrilun 2024 yana kan mulki.
INEC ta ce ragowar mazabun sun hada da Mazabar Kauran Namoda a jihar Zamfara, sai kuma mazabar Zariya Kewaye da Basawa a jihar Kaduna.
Sauran jihohin sun hada da Kogi, Anambra, Adamawa, Naija, Taraba da sauran su.
INEC tace za ta aika da ma’aikatan zabe 34,451 mazabun da za a gudanar da zabukan.
