Hukumar zabe me zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano ta bada takardar shairdar samun nasarar cin zabe ga ‘yan majalisun dokokin jihar nan 2, da suka samu nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a karshen makon daya gabata.
Kwamishinan hukumar zaben a nan Kano Abdu Zango shi ne ya mika shaidar lashe zaben ga wakilin kananan hukumomin Ghari da tsanyawa Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC, da Wakilin Bagwai da Shanono Ali Hassan Shanono na jam’iyyar NNPP a shalkwatar hukumar dake nan Kano.
A jawaban su daban-daban, zababbun ‘yan majalisar, sun yabawa kokarin hukumar zaben, bisa yadda ta jagoranci gudanar da zaben mai cike da gaskiya da dalci.
Sun kuma yabawa wadanda suka kada musu kuri’a, tare da shan alwashin sauke nauyin da suka dora musu musamman ta fannin harkar lafiya, ilimi, tsaro da kuma sama musu da tsaftataccen ruwan sha.
