Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) sun bukaci Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomi su dauki tsauraran matakai domin rage hauhawar farashi, duk da cewa ana samun wasu ci gaba a bangaren tattalin arziki a Nijeriya.
Manyan jami’an biyu, wato Babban Masanin Tattalin Arziki na Bankin Duniya a Nijeriya, Dokta Samer Matta, da Wakilin IMF a Nijeriya, Dokta Christian Ebeke, ne suka bayyana haka a Legas yayin taron hasashen tattalin arziki na 2026.
Inda Suka amince cewa gyare-gyaren tattalin arziki na haifar da ci gaba, amma sun jaddada cewa hauhawar farashi har yanzu na da yawa.
Dokta Ebeke ya gargadi Nijeriya kan yin sakaci da tunanin cewa a riga an kammala aiki, yana mai cewa komawa tsoma bakin gwamnati wajen daidaita farashi da kasuwa ba zai dore ba. Ya bukaci gwamnatocin tarayya da jihohi su tabbatar da ingancin kashe kudade domin amfanin ya isa ga rayuwar talakawa.
A nasa bangaren, Dokta Matta ya ce kodayake hauhawar farashi na raguwa, har yanzu babbar barazana ce ga jin dadin al’umma. Ya bukaci a mayar da hankali kan kashe kudi a bangaren jin dadin jama’a, musamman ilimi, lafiya da kariyar zamantakewa, yana mai cewa jihohi na da karin kudade kuma dole su yi amfani da su yadda ya dace.
