
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana ayyukan mazaɓu da ‘ƴan majalisar dokoki na ƙasa da na jihohi ke yi a matsayin tamkar fashi da rana tsaka ne.
Obasanjo ya bayayan hakan ne cikin sabon littafinsa da ya wallafa dake waiwaye kan makomar Najeriya la’kari da abubuwa na tarihi domin neman mafita a gobe.
Tsohon shugaban ya kuma bayyana ‘ƴan majalisar wannan jamhuriya a matsayi mafiya muni fiye da na jamhuriya ta farko da ta biyu.
Obasanjo mai shekara 88 ya ce, yana tuna wasu lokuta biyu da ya bata da ‘ƴanmajalisan ta ƙasa a lokacin yana shugaba, ya mulki Najeriya sau biyu; a lokacin soja da kuma farar hula.
“ƙudirin kafa hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ya shafe fiye da shekara guda da gaban majalisar kafin ta amince da shi”. In ji shi
Wannan ba hi ne karo na farko da tsohon shugaban kasar ke zargin ‘yanmajalisar ƙasar da wawure kudin ƙasar ba.
Obasanjo ya taba irin wannan kalamai a shekarar 2021 ma ya bayyanasu da ”marasa gaskiya kuma ƴan fashi” a wani taro da aka gudanar a Legas.