
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 (DISCOS) sun tara Naira biliyan 546 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025.
Hukumar ta kuma ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wutalanatarki ta kasa ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban.
Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.
Hukumar ta ce, abokan ciniki sun gaza biyan naira biliyan 190, na kuɗin wutar da aka lissafa musu, wanda hakan ya sa kamfanonin suka yi asarar naira biliyan 357, sakamakon rashin biyan kuɗin wutar.
A cikin rahoton zango na biyu na shekarar 2025, hukumar lantarkin ta ce jimillar wutar da dukkan kamfanonin suka samu a zangon na biyu ta kai ta naira biliyan 909, yayin da jimillar wutar da aka lissafa ta kai naira biliyan 742.
Rahoton ya ƙara da cewa, a cikin kamfanonin na Eko ne ya fi na ko ina wajen lissafin kuɗin wutar da kaso 96 cikin 100. Yayin da na Yola ya fi kowanne yin ƙasa da kaso 58.38 cikin 100.
Rahoton ya kuma nuna cewa kamfanonin rarraba lantarkin sun fi karkata wajen baiwa abokan ciniki na kasuwanci wuta a cikin zangon, inda suka fi tura wuta zuwa waɗannan rukunan fiye da masu amfani da ita a gidaje.
Sai dai rahoton ya ce kamfanin na shiyyar Fatakwal ne kaɗai ya rarraba wutar daidai da yadda hukumar ta amince a lokacin.