Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Tukur Buratai, ya ce akwai sanannun mutanen da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya, sai dai ya jaddada cewa ba shi ne ya kamata ya fito ya bayyana sunayensu ba.
Buratai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya ce
A cewarsa, “Ba ni ne zan dauki alhakin fadin sunayen masu daukar nauyin ta’addanci ba. Hukumomin da abin ya shafa sun san dalilan da suka sa ba a bayyana su ba. Wadannan mutane suna cikin al’umma kuma an san su.”
Ya kara da cewa alhakin da yake dauka ya ta’allaka ne kan wasu batutuwa da suka shafi rundunar sojin kasa kawai, ba dukkan al’amuran tsaro ba.
A baya, an rika matsa lamba ga gwamnati da ta fito da sunayen masu daukar nauyin ta’addanci, musamman bayan sanarwar da ta yi a shekarar 2021 cewa ta gano wasu mutane da kungiyoyi da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda.
Haka kuma, Hukumar NFIU ta taba bayyana cewa ta gano wasu kudade da ke da alaka da ayyukan ta’addanci, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike kan hanyoyin da ake bi wajen tallafa wa ‘yan ta’adda.
Sai dai har yanzu ba a bayyana sunayen wadannan mutane ba, lamarin da ke jawo suka daga kungiyoyin fararen hula da masana harkokin tsaro, wadanda ke ganin hakan na da muhimmanci wajen tabbatar da hukunta masu laifi.
Najeriya dai ta shafe fiye da shekaru goma tana fama da matsalar ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, inda kungiyar Boko Haram da bangarorinta suka yi sanadiyyar asarar rayuka da kuma raba dubban mutane da muhallansu.
