Hukumar Kwastam za ta rarraba shinkafa ga wasu ƴan Najeriya bayan ta kwace manyan tireloli maƙare da shinkafar a hannun yan fasakauri.
Kwanturolan Shiyar Kudu Maso Yamma, Shuaibu Muhammed Salisu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa RFI Hausa.
Ya ce shinkafar da aka kwace za a raba ta ga wadan da suka cancanta kamar ‘yan gudun hijira da sauran su bayan an tantance ingancin ta.
Shuaibu Muhammed Salisu har ila yau y ace hukumar ta kuma kwace kunshin miyagun kwayoyi da nauyin su ya kai kilogram 246,wanda ya ce su ne ke gurbata hankalin ‘yan bindiga da suka addabi kasar musamman yankin Arewa.
Hakan dai ya biyo bayan nasarar da hukumar ta samu na kwace haramtattun kayan da kudin su ya zarta naira biliyan daya da rabi da suka hada manyan tireloli makare da buhunan shinkafa da aka shigo da su kasar ta barauniyar
