
Daga Khalil Ibrahim Yaro
Hukumar Kashe Gobara Da Bada Agajin Gaggawa Ta Jihar Kano ta ja hankalin mazauna garin Doka dake karamar hukumar Tofa da su kula da irin yanayin da ke haifara da gobara.
Shugaban hukumar DSF Ibrahim Ibrahim bello ne ya Jagoranci Atisayen a yayin gudanar da taron wayar kan jama’a da Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar kano SEMA ta gudanar a garin.
Yayin da yake jawabi DSF Ibrahim Ibrahim Bello ya nuna mahimmancin kulawa da kai da kuma kiyayewa a konwane lokaci.
“A duk lokacin da gobara ta ritsa da kai to ka yi gagawar kwanta wa a kasa saboda illar hayaki. Domin a lokauta da yawa hayaki ne yake kisa ba wuta ba, amma kwanciyar a kasa zai baka damar tsiratar da kanka a lokacin da kake tafiya da rarrafe” in ji shi.
A nasa jawabin ASF 1 Abduljalil Muhammad Ishaq ya koyawa dalibai yanda za su kare kasansu idan an ce gobarar ta ritsa dasu a makaranta ko a gida “ a duk lokacin da gobara ta kama idan kasamu ka fito to kar ka yi nisa domin tsawarka a kusa ne zai bawa jami’an bada agaji damar ceto sauran da wuri.