Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta gargadi al’ummar jihar nan dasu kwacewa duk wani abun da ka iya jefa rayuwar su cikin hadari.
Darakta Janar na hukumar Alhaji Sani Anas Dakata ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai domin bayyana shirin da hukumar take a wannan lokacin na damuna.
Ya kuma yi kira ga iyaye dasu hana yaran nasu zuwa wanka cikin kudiddifai domin kaucewa daga samun asarar rayuka sanadiyar zuwan wankan.
Alhaji Anas Dakata ya bada tabbacin hukumar na ci gaba da wayar da kan al’umma mahimmacin tallafa wa hukumar a koda yaushe a aikin da suke yin a ceto rayuwar al’umma.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tace a shirye take a ko wane lokaci domin kai daukin gaggawa bayan faruwar wani iftia’in.
