Hukumar kashe gobara ta Kano za ta ɗauki ma’aikata sama da ɗari biyu tare da siyan sabbin motocin kashe gobara a shekara mai kamawa domin ci gaba da inganta ayyukanta a lungu da sakon jihar.
Daraktan Hukumar Sani Anas ne ya bayyana haka bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin majalisar dokokin Kano.
“Akwai kayayyakin aikin kashe gobara da dama da suka lalace a hukumar wanda duka za’a canza su da zarar an amince da kasafin da suka yiwa hukumar shekarar mai kamawa”. In ji shi.
Hukumar na daga cikin hukumomin gwamnatin jihar Kano da suke kare kasafin kudinsu kamar yadda aka saba.
