An gudanar da bikin shan fura ta duniya a garin Maliki inda aka yi shagalin shan fura da nono ba iyaka
Jama’ar Fulani daga cikin da kuma wajen Najeriya ne suka taru don tabbatar da wannan rana da aka ayyana da zama ta shan fura da nono a karo na farko kuma wacce kuma za a rika yi duk shekara.
An gudanara da biki ne a garin Maliki ta Tudun Wadan Karamar Hukumar Karo ta jihar Nassarawa a ranar Asabar.
An ayyana bikin ranar ne yayi daidai da bikin bude kasuwar shanu ta kasa da kasa da kuma bude masallacin Juma’a a na kasuwar.
Ga yadda da bikin ya gudana a cikin hotuna
Hotuna: Muslim Yusuf da Abubakar Usman (Dandalin HAFU 21st century Africa WhatsApp)