
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallar jana’izar Babban Malami na Madabo Malam Kabiru Ibrahim, a Kofar Kudu.
Daga nan aka wuce da shi zuwa makabartar Madabawa dake kusa da sansanin alhazai na jihar Kano, wato Hajj Camp, inda aka binne shi.
Sallar Jana’izar ta samu halartar dubban al’umma daga ciki da wajen jihar Kano.
Marigayi Malam Kabiru Ibrahim Babban Malami na Madabo, ya rasu a yammacin jiya alhamis yana da shekaru 80 a duniya, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ya shafe shekaru 30 akan kujerar Babban Malami na Madabo, kuma dan majalisar Sarki, inda ya shahara wajen bada fatawa a fadar Sarkin Kano
.