
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya aika da gudunmawar kudi miliyan 16 ga iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi.
Sanatan ya aika da manyan Jami’ansa karkashin jagoranci Farfesa Abdullahi bin Muhammad Shugaban Ma’aikatansa da kuma Honorabul Yusuf Tumfafi.
Sun kuma rarraba kudin miliyan daya lakadan gida-gida ga iyalan mamatan 16 a Kananan Hukumomin Rano da Bunkure da kuma Kibiya a ranar Asabar.
Sanata Barau ya yi alkawari taimakawa iyalan wadanda aka kashe ne ranar Laraba a yayinsu ziyarar jaje da ya je a garin Bunkure.
Ga yadda rabon ya kasance cikin hotuna


