Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya kuma ba su kyautar Naira Miliyan daya kowannensu baya ga kyautar alkyabba.
A ranar Alhamis ne zakarun musabaqar Buhari Sunusi da kuma Fatima Abubakar, suka kai wa sarkin ziyara a fadarsa tare iyayensu da malamai da kuma jagororin musabaqar.
Sarkin ya yi musu tarba ta girma da kuma karrama wa tare da ba su mazauni a kujerar alfarma ta kusa da shi wacce shugabannin kasashe da sauran manyan baki ne ke zama.
Sannan da kansa ya sa musu alkyabba don girmama wa baya ga kyautar Naira Miliyan daya kowannesu.
Ga yadda ziyarar ta kasance a cikin kayatattun hotuna:
Hotuna: Gems photography