
Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana dalilin ziyararsu ga shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje a ofishinsa a Abuja ranar Laraba.
Dan majalisa Rurum ya ce, ziyarar ta girmama wa ce ga shugaban jam’iyyar a matsayinsa na babba a jihar Kano kuma jigo daga jihar da suke wakilta a tarayya.
”Mun kai ziyara ta musamman ta ban-girma ga shi maigirma shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje
”Kuma dama muna da alaka ta kusa tsakaninmu illa al’amura na siyasa in ya taso akan iya samun bambancin ra’ayi ko da gida daya ake,” in ji shi.
Sun kuma yi hakan ne saboda lokaci ya fara kankama na tunkarar siyasar da ke tafe ta 2027, don haka suka fara tattaunawa, kamar yadda sauran ‘yan siyasa a matakai daban-daban na kasar suke ziyarce-ziyarce na neman shawara daga manya da hada tafiya da wadanda suke ganin za su kai ga cimma muradinsu na siyasa na jiha da kuma kasa, a matsayinsu na wakilan jihar ta Kano.
A hirarsu da BBC, Rurum ya ce, tattaunawarsu ta yi kyau kuma sun tsayar da lokacin sake ganawa domin ci gaba da ita kafin su fito da matsaya kan abin da suka zartar game da alkiblar da za su dosa a siyasarsu ta jiha da ma tarayya.
Rurum tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano ne kuma dan majalisar wakilai yana tare da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da danmajalisar wakilai Honorabul Ali Madaki da kuma tsohon dan majalisar tarayya wakilai Badamasi Ayuba
Ana kallon wannan ganawa da shugaban jam’iyyar APC a matsayin wani shiri na sauya sheka daga jam’iyyarsu ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.