
Hukumar Hisbah karkashin ‘Operation Kauda Badala’ ta gano wani gidan siyar da abincin da ake zargin ana aikata badala a unguwar Ja’en da kuma Gaida.
Haka kuma hukumar ta yi nasarar cafke wasu mutane hudu, biyu maza, biyu mata a wadannan gidaje.
Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dakta Mujahiddeen Aminudeen, ya shaidawa premier Radio cewa suna zargin wata baiwar Allah da fakewa da sayar da abinci wajen kulla aikata badala.
Ya ce hukumar na ci gaba da fadada bincike, kuma da zarar sun kammala zasu maka mutanen da aka kama a gaban kotu.
Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dakta Mujahiddeen Aminudeen ya jan hankalin iyaye wajen ci gaba da sanya ido kan yaransu, musamman ma mata.