
Indiya da Pakistan sun dakatar da bayar da izinin shiga da fita (Biza) a tsakaninsu sakamakon tsamin dangantaka a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.
Matakin na zuwa ne bayan da India ta zargi Pakistan da hannu a harin ‘yan bindiga da ya hallaka mutane 26 yawancinsu ‘yan yawon bude ido a yankin Kashmir wanda kasashen biyu suka dade suna takaddama a kansa.
Hukumomin India sun ce daga ranar lahadi za su dakatar da bayar da biza da kuma soke dukkan wacce suka bai wa ‘yan Pakistan tare da umartar duk ‘yan Pakistan da a suke cikin India su bar kasar kafin karewar wa’adin Bizarsu.
Kasar ta kuma sanar da daukar wasu matakai da suka hada da rage yawan ma’aikatan diflomaisyya da kuma rufe kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A nata bangaren Pakistan ta rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen sama mallakar Indiya tare da dakatar da dukkan harkokin kasuwanci da Indiya.