
Ministar Masana’antu Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta bayyana damuwa kan karin harajin da Amurka ta sanya kwanan nan, tana mai cewa matakin zai haifar da koma baya ga tattalin arzikin Najeriya da kuma dangantakar cinikayya tsakanin kasashen biyu.
A cewar Ministar, karin harajin zai shafi fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Amurka kai tsaye, inda ta bayyana cewa a kowace shekara, Najeriya na fitar da kayayyaki da darajarsu ke kai dala biliyan 5 zuwa 6 zuwa kasuwar Amurka.
Sannan kuma Karin haraji na iya bai wa kasashen da ke gogayya da Najeriya damar mamaye kasuwar, lamarin da zai rage karfin Najeriya a fagen cinikayya.
Don kaucewa illolin wannan mataki, Ministar ta ce, an fara tattaunawa da ofishin jakadancin Amurka da kuma kungiyar WTO domin samar da mafita. Ta kuma jaddada cewa Najeriya ba za ta zuba ido a ci galabarta a kasuwar duniya ba.