
Daga Khalil Ibrahim Yaro
‘Yan kungiyar ‘The Buhari Organization’ sun ce har yanzu kungiyar su tana nan ba ta mutuwa ba, kuma suna nan akidarsu ta Najeriya sai mai gaskiya.

Shugaban kungiyar karkashin jagorancin Malam Isiyaku Musa ne suka bayyana aka a wata ziyara ta musamman da suka kawo suka Premier radio a ranar Talata.
Shugabannin bayana cewa suna nan akan doron tsarin da suke bi tun asali, wannan ce tasa sukai tattaki har gidan radion a wani yanayi na kula kyakyawar alaka tsakanin su da al’umma.
“Kungiyarmu na nan babu inda ta je, kuma a bisa akida ta Najeriya sai mai gaskiya duk da aabin da ya faru a mulkin tsohon shugaba Buhari. Sai dai a wannan karon mun fito da wanni tsari da sai sun tatance wanda za mu goyawa baya.
“Mu babu ruwanmu da jami’yya a kowanne bangare mutum nagari ya ke mai nagarta za mu goya masa baya matukar ya cancenta. Kuma structure dinmu tana nan tundaga sama hara kasa”. In ji shi.

Hajiya Rabi Ibrahim ita ce shugabar mata a kungiyar a nata jawabin ta ce “duk ‘ya’yan kungiyar shirye muke mu sake fitowa don ceto kasar nan daga halin da take cikin duk da akasin da aka samu a baya lokacin Buhari da muka goya masa baya”.