Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hakurin da suke yi na sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi ba zai tafi a banza ba.
Shugaban yayfadi haka ne a Majalisar Kasa a ranar Laraba a yayin da gabatar da kasafin kudin shekarar 2025
Tinubu ya yarda cewa shekara daya da ‘yan watanni da gwamnatinsa ta yi sun kasance masu wuya ga ‘yan Najeriya, amma su ci gaba da hakuri sauki na tafe.
“An sha wahalhalu. Kuma hakan ba zai tafi da banza ba. Dole ne mu ci gaba da amincewa da tsarin domin cikar burinmu.
“Aikin bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaba wadanda muka fara watanni 18 da suka gabata na ci gaba da tafiya,” in ji shi.
Domin babu wata hanya da ta dace ta farfado da tattalin arzikin kasar sai ta hakan wanda “hanya ɗaya ce da dole muka ɗauka domin Najeriya ta samu damar zuwa wani babban mataki”. Inji shi.
Sananan ya ce, hanyar gyaran a yanzu na samar da kyakkyawan sakamako sosai, kuma a matsayina na shugaban wannan ƙasa mai albarka, ya san cewa wannan hanya ba mai sauƙi ba ce.
Tinubu ya gode wa ‘yan Najeriya da kasance wa tare da gwamanatinsa a wannan mataki na tafiya domin gyara.
Shugaban ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 ga majalisun dokoki ƙasa.
Kasafin kuɗin, kamar yadda ya bayyana, na nufin ɗorawa kan ayyukan da gwamnatinsa ta faro watanni 18 da suka gabata.