
Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Kano ta sanya Miliyan Takwas da Dubu Dari Biyar 8,500,000 a matsayin kudin ajiya ga maniyyata hajjin 2026 mai zuwa.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar Sulaiman Dederi ya aikewa manema Labarai ya ce, wannan na zuwa ne jim kadan bayan umarnin da Hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta bayar ga jihohi da su fara karbar kudin ajiyar daga masu niyyar zuwa Hajji a shekarar 2026.
Babban daraktan hukumar a nan Kano Alhaji Lamin Rabi’u ne ya tabbatar da hakan, yayin wani taro da ya gudanar da mambobin hukumar da ma’aikatan gudanarwa da jami’an cibiyoyin hajji na kananan hukumomi da kuma sauran ma’aikatan hukumar a ofishinsa.
“An warewa Jihar Kano kujera dubu biyar da ɗari shida da tamanin da huɗu (5,684) don Hajjin shekarar 2026, kuma za’a fara karɓar ajiya nan take, kuma za a cigaba da karɓa har zuwa ranar 5 ga Oktoba, 2025, wanda a ranar za a sanar da cikakkum kuɗin aikin hajjin”. In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya kuma buƙaci duk masu niyyar zuwa hajji da su gaggauta biyan kuɗin ajiya da wuri, daidai da jadawalin da Masarautar Saudiyya ta bayar na Hajjin 2026. Haka kuma, ya jaddada cewa masu niyyar hajji dole ne su mika ingantaccen fasfo na ƙasa da ƙasa a matsayin wani ɓangare na rajistar.