
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala rijistar maniyyata 3,155 da za su gudanar da aikin Hajjin 2025.
Darakta hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbaffa ne ya sanar da hakan yayin karbar bakuncin tawagar Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Kasa a ofishinsa a ranar Alhamis.
Shugaban ya kuma bayyana irin shirye-shiryen da suke yi wa maniyyatan.
“An kammala shirye-shiryen da suka shafi takardu da jakunkunan hannu na maniyyatan yayin da ake ci gaba da kammala hada bizar su”. In ji shi.

Alhaji Laminu ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayan da take bai wa hukumar domin saukaka tafiyar da al’amuran Hajji.
A nata bangaren, Shugaban hukumar shige da fice na filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Aisha Shehu, ta ce ziyarar su na nufin karfafa hadin gwiwa don saukaka aikin Hajji.