
Gwamnatin tarayya ta ce ba ta sa hannu kan wata yarjejiya tsakanin ta da kungiyar malaman jami’a ta kasa ASUU ba.
Ministan Ilmi Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin tarayya Abuj
Dr. Alausa Yace an dai kafa kwamitin mutane 7 karkashin jagorancin Babban sakataren ma’aikatar Ilmi Abel Enitan wanda zai gabatarwa gwamnati takardun yarjejeniyar domin yin duba kan a su.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar ASUU ta kauracewa taron ta da gwamnatin tarayya da aka tsara yi a jiya Alhamis, in da shugaban ta Farfesa Chris Piwuna yace ba su samu gayyata a hukumance daga gwamnati ba.
Kungiyar ASUU din dai ta ce gwamnati ta gaza cimma yarjejeniyar dake takanin su ta 200