Ministan Lantarki a Najeriya ya ce Adebayo Adelabu ya ce gwamnatinsu na shirin karɓar rancen dala miliyan 190 daga Japan domin “inganta ɓangaren makamashi mai dorewa”.
A cewar wata sanarwa daga ma’aikatarsa ajiya Asabar, ministan ya bayyana haka ne yayin taron ƙasashen Afirka da Japan da ke gudana a birnin Yokohama.
Ma’aikatar ta ce tawagar wakilan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta tattauna da kamfanoni a ɓangaren lantarki da makamashi.
Da yake magana yayin taron, Mista Adelabu ya ce hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA) ce za ta bayar da lamunin, inda shirin zai samar da makamashi maras gurɓata muhalli ga yankunan da ba su fiya samun sa ba a Najeriya.
