
Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa (NLC) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ya isa wajen tafiyar da lamarin yau da kullum na ma’aikaci .
A cewarsu tashin farashin kayan abinci da sufuri da haya da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar rayuwa.
A wasu jihohi kamar Imo da Legas da Ribas sun riga sun ƙara mafi ƙarancin albashi sama da wanda gwamnatin tarayya ke biya.
Mista Benson Upah, Sakataren riƙo na NLC, ya ce, hakan ya zama dole.
“Naira 70,000 ba za ta iya ɗaukar nauyin rayuwa a wannan yanayi na tattalin arziƙi da ake ciki ba”. In ji shi.
Shi ma shugaban ƙungiyar manyan ma’aikata, Mista Shehu Mohammed, ya jaddada buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa kan lamarin.
“Ma’aikata na buƙatar gwamnati ta ƙara albashi tare da aiwatar da manufofin da za su rage tsadar rayuwa a Najeriya”. In ji shi