
Gwamanatin tarayya ta kaddamar da wani shiri na musamman karkashin ma’aikatar lafiya ta kasa domin fara dakko marasa lafiya daga gida.
Da yake kaddamar da shirin wakilin ministan lafiya na kasa Dr. Sa’id Ahmad Tumbolwa ya ce duba da yadda kasashen ketare ke kula da tsarin kiwon lafiya yasa gwamanatin tarayya samar da motacin agajin gaggawa da zasu rika dakko marasa lafiya daga gida domin ganin a karfafa fannin na lafiya a fadin kasar nan.
Sa’id Ahmad Tumbolwa ya kuma kara da cewa wannan tsarin zai taimaka matuka wajen rage yawan mutuwar masara lafiya.
Shima ana sa jawabin shugaban Asibitin Koyarwa na Aminu Kano farfesa Abdurrahman Abba Sheshe cewa yayi duba da yadda shugaban kasa ya damu da afannin lafiya yasa aka kawo tsarin na dakko mara lafiya daga gida zuwa a sibiti a kyauta.
Wakilinmu Mustapha Muhammad kankarofi ya rawaito cewa shirin zai zama wani mataki na bunkasa fannin lafiya tare da samar da sauki ga marasa lafiya domin zuwa asibiti akan lokaci.