
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya Amnesty International, ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyar jama’a, musamman a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.
Wannan zargi na zuwa ne a matsayin martani kan rahotannin kisan gilla da wasu ’yan bindiga suka kai a jihar Zamfara, inda aka hallaka akalla mutane 20 a wani sabon hari.
Shugaban Amnesty International a Najeriya Isa Sanusi ya bayyana cewa, akwai koma baya da gazawa a dabarun da gwamnati ke amfani da su wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar.
A cewarsa, harin na Zamfara ya sake tona alfanu game da irin sakacin da ke tattare da tsarin tsaron Najeriya.
“Yayin da ’yan Najeriya ke fuskantar barazana ga rayukansu kullum, ’yan siyasa sun fi mayar da hankali kan shirye-shiryen zaben 2027 maimakon tabbatar da tsaron al’umma,” in ji Sanusi.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya na da nauyin kare ’yan kasa daga hare-hare da kisa, tare da tabbatar da cewa al’umma na cin amfanin shugabanci.
Kungiyar ta kasa da kasa ta bukaci daukar matakan gaggawa don dakile irin wadannan hare-hare da suka zama ruwan dare a jihohin Arewa.