
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa fiye da mambobin Katsina Community Watch Corps 100 da kuma fiye da ’yan sanda 30 sun rasa rayukansu yayin yaki da ’yan bindiga a jihar.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na Ciki da Harkokin Gida, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana hakan don karyata labaran karya da ke yawo a kafafen sada zumunta, yana mai jaddada cewa an samu ci gaba tun bayan hawar Gwamna Dikko Umaru Radda a 2023, lokacin da dukkan kananan hukumomi 24 ke fama da hare-hare.
Ya ce yanzu wasu sun koma hayyacinsu, ciki har da Danmusa, Jibia, Batsari da Charanchi, saboda hadin gwiwar hukumomin tsaro.
Yace gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa iyalan wadanda suka mutu da wadanda abin ya shafa, tare da kira ga jama’a da su hada kai, su kasance masu lura.
https://shorturl.fm/G94gh