
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin daukar nauyin karatun ‘Yan tagwayen jihar Kano da aka haifa a manne bayan da kasar Saudi Arabia ta yi nasarar kammala aikin rabasu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya tarbi tagwayen a filin tashin jirage na Malam Aminu Kano bayan da hukumar Kasar Saudi Arabia ta dawo dasu gida jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin jihar Kano zata dauki nauyin karatunsu har zuwa jami’a tare da ci gaba da kula da dawainiyar lafiyarsu da ta iyayensu.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnati zata samar da wani tsari da zai tabbatar da dorewar kula da tagwayen koda bayan kammala gwamnatinsa.
Ya godewa gidauniyar Sarki Salman bin Abdul’aziz da ofishin jakadancin Kasar Saudiyya bisa daukar nauyin gudanar da aikin.
Da yake jawabin godiya mahaifin tagwayen Hassan Isah ya godewa Kasar Saudi Arabia bisa aikin da aka yi musu kyauta da kuma kyakkyawar kulawar da aka basu a yayin zamansu a kasa mai tsarki tsawon shekaru biyu.
Haka zalika ya godewa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa kyakkyawan jagorancinsa da bibiya domin tabbatar da an yi aikin cikin Nasara.
A watan Oktoban shekarar 2023 ne Kasar Saudi Arabia ta dauki nauyin aikin raba yan tagwayen mata Hassana da Hussaina wanda aka haifa a manne inda suka shafe tsawon shekaru biyu a kasar ana kula da lafiyarsu.