Gwamnatin Kano ta ce ta ware Sama da Naira miliyan dubu uku domin biyawa dalibai ‘yan asalin jihar wadanda suka samu Credit 5 a jarrabawar su ta Qualifying kudin rubuta jarrabawar NECO, NBIAS da NABTEB.
Kwamishinan ma’aikatar ilimi ta Kano Alhaji Ali Haruna Makoda ne ya tabbatar da hakan taron manema labarai da ya Kira.
Kwamishinan yace daga cikin Dalibai 141,715 da suka rubuta Jarabawar ta Qualifying domin neman cancantar gwamnati ta biya musu jarrabawar NECO, NABTIP da NBAIS, kaso 75 cikin 100 ne suka yi nasarar samun Credit 5 wanda za ta dauki nauyin su koda basu ci turamci da lissafi ba.
Daliban da zasu amfana da kuɗin tallafin sun hada da wadanda zasu rubuta jarabawar NECO, NAPTIB da NBAIS, inda kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin ta Kano biyawa kowane dalibi dukkan abinda za’a bukata game da jarrabawar uku tare da horan iyayen yara da su kai karar duk shugaban makarantar da bukaci su bada kudi akan sha’anin jarrabawar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar kwamishina Makoda Na cewa biyawa daliban jihar nan kudin jarabawar, yana daga cikin burin gwamnati na inganta ilimi a Kano.
