Gwamnan Kano ya karbi belin mata 8 dake tsare a gidan gyaran hali na Goron Dutse.
Cikin wadanda aka saki akwai masu juna biyu mutum biyu da masu shayarwa biyu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi daurarrun yayin ziyarar bazata da yakai Gidan kurkukun.
Da yake jawabi Gwamnan ya ce ya kai ziyarar ne domin duba halin da daurarrun suke ciki.
Ya nuna damuwar sa bisa yawan daurarrun da suke jiran hukunci, yana mai cewa cikin daurarru 1,939, guda 382 kawai aka yiwa hukunci yayin da 1,536 ke cigaba da jiran hukunci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnati zata hada gwiwa da bangaren shari’a domin rage cinkosan gidajen yari.
