
Babban mai taimaka wa gwamnan Kano wajan dauko rahoto a hukumar yawon bude ido ta jihar Kano Ibrahim Adam Bagwai, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, daga cikin otal din da jami’an hukumar suka rufe sun hadar da Sarina Suites, Horizon Hotel, Blue Spot Hotel, da wasu otal guda bakwai da ke jihar Kano.
Sanarwar ta ƙara da cewa, matakin na cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa cibiyoyin yawon buɗe ido da kuma otal din sun bin ƙa’idojin gwamnati da kuma kare mutuncin al’umma.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da sa ido kan dukkan otal otal da kuma wuraren shaƙatawa da ke jihar domin tabbatar da tsabta, tsaro da bin ƙa’idojin da aka kafa.