
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci hadin kan kungiyoyin Fulani da manoma, don ciyar da jihar gaba, ta hanyar bunkasa bunkasa harkokin noma da kiyo.
Mai taimakawa Gwamnan Kano kan harkokin da suka shafi kungiyar Fulani ta FULDAN, Rukayya Umar Gadon Kaya ce ta bayyana hakan, a taron wayar da kan Fulani da manoma, kan hanyoyin magance sabanin da ake samu tsakanin Fulani da manoma.
Rukayya Umar Gadon Kaya ta ce, a yanzu haka, Gwamnatin Kano na bakin kokarinta wajen ganin ta samarwa Fulani da manoma hanyoyin da zasu kara bunkasa harkokinsu.
A nasa jawabin shugaban kungiyar Fulani ta FULDAN reshen Kano Sani Adamu Dakata, Kira yayi ga Gwamnan Kano da ya sanya ido kan wasu bata gari da suke kokarin kawo sabani tsakanin Fulani da manoma.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a bangarori daban-daban, inda aka tattauna kan hanyoyin magance rikice-rikicen da ake samu tsakanin Fulani da manoma a wasu yankuna.