
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokokin kirkirar sabbin Hukumomi guda hudu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana a Yawun Gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
Sabbin hukumomin da gwamnana ya sanya wa dokokinsu hannu sune ne Hukumar Bayar da Kariya ta Jihar Kano (KASPA) da Hukumar Kula Da Alluna da kuma Tallace-Tallace ta jiha (KASIAA) da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Bayanai ta Jihar Kano (KASITDA) da kuma Hukumar Raya Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu ta Jihar Kano (KASMEDA).
“Sabbin hukumomin za su samar da guraben aiyukan yi da jawo hankalin masu zuba jari da ma kara inganta nagartan manufofin gwamnatin jihar ta yadda jihar za ta zama cibiyar fasahohi da sana’o’I”. In ji gwamna a yayin bikin sa hannun
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi ga jama’ar jihar kan bijirewa dokokin da suka kafa sabbin hukumomin, ya kuma ba da tabbacin cewa duk mai kunne kashi zai fuskanci hukunci domin gwamnatin sa ba za ta daga wa masu bijirewa dokar kafa ba.