
Gwamnatin jahar Kano ta jaddada aniyarta na ci gaba da tallafawa Mata da Matasa a fadin jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara Da ci gaban Al’umma Dakta Abdulkadir Abdussalam ne ya bayyana hakan yayin ziyarar Kananan Hukumomin Dala da Gwale.
A ci gaba da kai ziyarar da yake yi a Kananan Hukumomi 44 da na fadin jihar.
A ziyarar wanda ya Samu Wakilcin Babbaban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Musbahu Ahmad Badawi ya ce, Mata da Matasa na da Kyakkyawar rawar takawa wajen cigaban al’umma.
“Nan bada dadewa ba Gwamnatin Kano za ta samarwa da mata da Matasa Sana’oi domin Samun dogaro da Kan su”. In ji shi.
A jawabinsa na maraba, shugaban Karamar Hukumar Dala, Alhaji Surajo Ibrahim Imam da takwaransa na Gwale Alhaji Abubakar Mu’azu MOJO, sun bayara da tabbacinsu na bayar da gudunmawa domin Samun nasarar gudanar da shirin Kamar yadda ya dace.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin Sanarwa Jamiin Yada Labarai Na Ma’aikatar Raya Karkara, Faruk Ghali Masanawa.
Jami’Iin ya kuma ce, Hakimin Dala Alh. Aliyu Harazimi, Dan Amar Kano da na Gwale Alh Alh Mahmud Ado Bayero, bayar da tabbacinsu su ka yi wajen bayar da gudunmawar su ako da yaushe.