Gwamnatin Kano ta dauki sabbin ma’aikata 120 a hukumar tattara haraji ta jihar, da nufi samar da karin kudin shiga, da samawa matasa ayyukan yi.
Da yake bayar da takardun aikin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada wa sabbin ma’aikatan kudirin gwamnatin sa na karfafa hanyoyin tattara haraji domin bunkasa kudin shiga ta yadda gwamnati zata samu sukunin gudanar da ayyukan ci gaba yadda ya kamata.
Gwamnan ya kuma bukaci sabbin ma’aikatan da su kasance masu gaskiya, rikon amana da bin ka’idojin aiki, domin cimma manufofin da aka dora wa Hukumar Tattara Harajin ta Kano.
A nasa jawabin Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kano, Dr Zaid Abubakar, ya bayyana cewa daukar sabbin ma’aikatan zai taimaka matuka wajen inganta ayyukan hukumar da kara yawan kudaden haraji da jihar ke samu.
