Gwamnatin Jihar Kano ta dage gudanar da aikin tsaftar Muhalli na wata-wata da aka saba gudanarwa a duk ranarkun Juma’a da Asabar na karshen wata.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Muhalli ta jihar Isma’ila Garba Gwammaja ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a.
Ma’aikatar Muhallin ta tabbatar da cewa za’a gudunar da aikin tsaftar muhallin a mako mai zuwa kamar yadda aka saba.
Gwamnatin Kano ta ware Juma’a ta ko wacce karshen wata domin tsaftar tashohin Mota da Ma’aikatu da kuma hukumomin gwamnati wanda kuma asabar ta zama ta kowa da kowa.
Ana hasashen dagewar ta wannan watan ba zai rasa nasaba da taron maulaud da na mabiya darikar Tijjaniyya za su yi ba a babban birnin jihar a ranar Asabar
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II shine halifan shugaban darikar a Najeriya