Gwamnatin jihar Sokoto ta soke duk wasu takardun mallakar gidaje ko fili da gonaki a fadin jihar tun daga lokacin da aka kirkireta zuwa yau, bayan shekaru 50 ko fiye da haka da suka gabata.
Gwamnatin ta bai wa al’ummar jihar wannan wa’adin na watanni 4 domin sabunta takardun mallakarsu.
Alumma dai sun bayyana mabambantar ra’ayoyinsu game da wannan yunkuri. Inda was uke gannin hakan zai taimakawa gwamnati wajen tantance mamallakan filaye yayin da wasu kuma ke ganin yunkuri zai kuntatawa alumma duba da halin da ake ciki na matsaloli irin na tattalin arziki da tsaro.
Tuni dai wasu da abin ya shafa suka garzaya kotu domin kalubalentar wannan mataki na gwamnatin jihar ta Sokoto.
