Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayar da umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar ba bisa ƙa’ida saboda alaƙar hakan ke da shi wajen aikata laifukan da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Gwamnan ya kuma ce yawan baƙi da ke shiga yankunan da ake haƙar ma’adanai na ƙara haddasa matsalar tsaro.
Domin shawo kan matsalar, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai binciki waɗanda ke da izinin haƙar ma’adanai da kuma ƙirƙirar tsarin kula da ayyukan haƙar.
Gwamnan ya ƙara da cewa za su yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da tsare-tsaren doka da kuma inganta matakan tsaro.
Gwamnan ya yi alƙawarin duba matsalar tsaro a yankunan da ake haƙar ma’adanai gaba ɗaya tare da tabbatar da cewa kamfanonin haƙar ma’adanai suna taimaka wa al’ummomin yankunan da suke aiki a cikinsu.
