Ma’aikatar lafiya ta Jihar Jigawa ta ce ta sa hannu tsakaninta da wasu kungiyoyi masu taimakawa masu lalurar gani domin dawo musu da lafiyar idanunsu a wani bangare na inganta fannin lafiya a Jihar.
Kwamishinan lafiya na Jihar Muhammad Abdullahi Kainuwa ne ya bayyana haka a yayin zantawarsa da wakilinmu Mustapha Muhammad Kankarofi a juma’ar da ta gabata.
Ya ce an gina sashin kula da lafiyar idanu a wasu daga cikin manyan asibitocin Jihar domin taimakawa masu matsalar gani.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa ko a kwanakin nan ma’aikatar lafiya ta gudanar da aikin idanu ga mutane 189 a karamar hukumar Ringim da mutane 200 a karamar hukumar Gumel.
Muhammad Abdullahi Kainuwa yace gwmanatinsu za ta ci gaba da kokari wajen bunkasa kiwon lafiya a jihar Jigawa baki daya.
