
wamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da shirin noman rani a Lallashi ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari.
Wannan wani bangare ne na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar al’ummar jihar
Da yake jawabi lokacin kaddamar da aikin, Gwamna Umar Namadi yace,
“Wannan na a matsayin wata hanya ta jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an samar da abinci mai yalwa da samar da hanyoyin rayuwa mai dorewa da rage radadin talauci a tsakanin al’umma”
Ya kara da cewa, babban abin da gwamnatinsa ta sanya a gaba shi ne na cimma manufofin kudirorinta 12 wajen amfani da hanyoyin noma na zamani a Jihar Jigawa, musamman ta hanyar gudanar da ayyukan noma a duk shekara.
Gwamna Namadi ya ce, gwamnatinsa na daukar matakai daban-daban don gyara da fadada wuraren noman rani a fadin jihar da suka hada da samar da madatsun ruwa da rijiyoyin burtsatse na yau da kullum.

Sai dai an bayyana cewa shirin noman na Lallashi da rijiyar burtdatse ya kunshi gonaki hekta 10 kuma yana samun tallafin manyan rijiyoyin burtsatse irin na masana’antu guda hudu, kuma ya zuwa yanzu, manoma sama da 80 ne ke cin gajiyar shirin kai-tsaye, wanda ake sa ran zai bunkasa noman sosai da kuma yaukaka tattalin arziki.
Da yake jawabi a madadin manoman yankin, malam Aliyu Musa ya ce,
“Abin da gwamnati ke yi wa al’ummomin da ke kewayen wurin noman rijiyoyin burtsatse tamkar jari ta bayar na rayuwa da ba za a iya tantance adadinsa ba”.
A cewarsa, jama’a za su ci gaba da addu’o’in samun nasarar shirin tare da fadada shi a yankunan jihar gaba ɗaya.