
Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da rabon kayan noma na Naira biliyan 1.5 don shirin ba da lamuni na noma kashi na biyu ga ma’aikatan gwamnati.
An fara shirin ne a shekarar 2024 inda jihar ta amince da Naira biliyan 3, wanda ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a 8,828 suka amfana da shirin.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da rabon kayan a Dutse, babban birnin jihar, Gwamna Umar Namadi, wanda mataimakinsa, Engr. Aminu Usman ya wakilta, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati ba sai ta hanyar albashi kadai ba.