Shugaban Majami’ar ECWA ya yi kira ga gwamanti da ta kara matsa kaimi kan matsalar tsaro.
Shugaban Majami’ar ta Kano Rabran Dakta Emmanuel Malomo ya ce, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tashi tsaye domin kawo karshen matsalar tsaro.
Malomo Ya bayyana hakan a hirarsa da Premier radio, jim kadan bayan kammala wani taron shekara shekara da aka yiwa take da suna nuna godiya ga Allah da aka gudanar
Gwamnan Kaduna ya koka kan siyasantar da harkokin tsaro
Tinubu Ya Sauke Babban Hafsan Tsaron Najeriya
Harin ‘yan ta’adda: Shugaban Ƙaramar Hukumar Shanono Yajinjinawa Jami’an Tsaro
“Hada hannu da masu ruwa da tsaki ta ko wacce fuska zai taimaka wajan kawo karshen yan bindigar da suka addabi al’umma”. In ji shi.
A Jawabinsa a taron, Rabran Dakta Haruna Abdu Tukura daga jihar Filato, ya bayyana mahimmacin taron da kuma abin da suke fata a shekarar 2026 mai zuwa.
Daga bisani mabiya addinin kiristanci sun gabatar da addu’oi na musamman domin samun zaman lafiya a nan jihar Kano da kasa baki daya.
