Hukumar Tattara Kudin Haraji ta jihar Kano ta garkame ofisoshin Kamfanonin gine-gine na Dantata da na jirgen saman Max Air da kuma wasu kamfanin guda biyu a bisa laifin kin biyan haraji.
Daya babban kamfanin da ta rufe shine kamfani sarrafa shinkafa na Northern Rice and Oil Milling dake rukunin manyan masana’antu na Gunduwawa da ke jihar.
An rufe kamfanonin ne a bisa laifin kin biyan haraji ga gwamnatin na tsawon wasu shekaru da yawansu ya kai na miliyoyin Naira.
Gwamnati na bin kamfamin Max Air bashin harajin shekara biyar, yayin da aka rufe kamfanin gine-gine na Dantata and Sawoe bashin harajin ma’aikata na shekarun 2021 zuwa2022 da ya kai jimlar Naira 241.2 Miliyan
A jawabinsa ga manema labarai Jami’in hukumar Ibrahim Abdullahi da ya jagoranci rufe kamfanonin ya ce, daukar wannan mataki ya zama dole la’akari da yadda kamfanonin suka yi kememe wajen sauke hakkin jihar na haraji da ke kan su.
Ya kuma ce kamfanoni za su cigaba da zama a rufe har sai sun biya harajin ga gwamnati.