Aminu Abdullahi Ibrahim
Kwamishinan lafiya Abubakar Labaran Yusuf, ya ce duk wata gwamnatin jihar Kano na kashe Naira miliyan 55 wajen sayen kaya na masu haihuwa da awo.
Kwamishinan ya bayyana hakane yayin sake bude Asibitin Nuhu Bammali dake Kofar Nasarawa a Alhamis din nan.
Bayan sake bude Asibitin gwamnatin jiha ta samar da sabbin kayayyakin aiki da magunguna da likitoci da zasu kula da mata da kananan yara.
Abubakar Labaran Yusuf, ya ce a watan Oktoba da ya gabata sun samu mata masu haihuwa guda dubu 5,425.
Ya kara da cewa sun yiwa masu juna biyu guda 399 aikin tiyata wajen haihuwa sai masu zuwa awo fiye dubu 32, 47.
Abubakar Labaran Yusuf, ya kuma ce matan da suka haihu da kansu sun kai kimanin dubu 5,275, yana mai cewa asibitoci 52 suke baiwa kayan kula da lafiya duk wata.
Abubakar Labaran Yusuf, ya kara da cewa Asibitin Nuhu Bammali shine na biyu a jihar Kano wajen karbar mata masu juna biyu da kananan yara bayan Asibitin Murtala.
Da yake bude Asibitin gwamnan na Kano ya ce gwamnatin sa zata cigaba da samar da abubuwan da zasu inganta kiwon lafiya musamman asibitocin mata da kananan yara.
Ya ce sun bayar da kwangila daban daban tabyin gyare-gyare a asibitocin birane da karkara wanda tuni an fara aikin wasu.
Abba Kabir Yusuf, ya bukaci mata da za su amfana da gyaran Asibitin na Nuhu Bammali su rinka kulawa kayan da aka samar da tsaftar Asibitin.
Hakazalika ya yi kira gare su su yi amfani da magunguna da kayan aikin da aka samar yadda yakamata.