
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga dukkanin jami’an gwamnati da su kasance masu adalci wajen rike amanar ma’aikatun da suke jagoranta, domin dakile cin hanci da rashawa a hukumomi da ma’aikatu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kammala taron bita na kwanaki uku da aka shirya ga dukkanin jami’an gwamnati, wanda ya gudana a jihar Kaduna ranar Lahadi.
Ya ce manufar taron ita ce kara inganta nagartar shugabanci da kuma baiwa jami’ai damar fahimtar rawar da ya kamata su taka wajen gudanar da amanar da aka dora a wuyansu.
Ya ce gwamnati ba zata lamunci cin hanci da rashawa a kowanne mataki ba, saboda haka akwai bukatar kowane jami’i ya tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gudanar da ma’aikatun da ke karkashin jagorancinsa.
Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya ido a kan dukkanin ma’aikatu da hukumomi domin tabbatar da cewa an gudanar da ayyuka yadda ya kamata ba tare da nuna son rai ba.
Haka kuma ya jaddada muhimmancin gaskiya, rikon amana da shugabanci nagari a matsayin ginshikan da za su tabbatar da dorewar ci gaban jihar Kano tare da samar da walwala ga al’umma.
Gwamnan ya yi kira ga jami’an da suka halarci taron bita da su yi amfani da abin da suka koya wajen inganta ayyukan gwamnati, tare da kasancewa jakadu na gaskiya da amana a duk inda suka tsinci kansu.