
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da ƙarin sabbin jami’an tsaro guda 200 domin ƙarfafa tsaron al’umma a fadin jihar.
A cikin sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar ta Katsina, Malam Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, ya ce, sabbin jami’an rukuni na uku ne da aka kammala basu horo.
Kuma za a tura su zuwa ƙananan hukumomin Kankia da Dutsinma, inda kowace za ta karɓi jami’ai guda 50.
Gwamna Radda ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan da ake fama da hare-haren ’yan bindiga.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ba za ta tattauna da ’yan bindigar ba, sai dai za ta ci gaba da mara baya ga yarjejeniyar sulhu ta al’umma da ke gudana a wasu yankunan.