Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya aike wa majalisar dokokin Kano sunan Shehu Wada Sagagi da sauran wasu mutane 5 domin ta amince masa ya nada su a matsayin kwamishinoni.
Wakilinmu ya rawaito cewa, hakan ta bayyyana ne a yayin da Kakakin Majalisar Jibril Isma’il Falgore ya karanto wasikar da aiko wa majalisar na bukatar tantace su domin nada su makaman.
Sauran wadanda aka aika da sunayensu sune
1. Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya
2. Dakta Isma’il Dan Maraya
3. Dakta Dahiru Mohd Hashim
4. Dakta Injiniya Gaddafi Sani Shehu
5. Abdulkadir AbdulSalam.
Shehu Wada Sagagi shine tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar wanda aka sauke da kuma kawar da aikin ofishin baki daya a wani garanbawul da gwamnan ya yi wa Majalisar Zartarwar Jihar a makon jiya.
Daga baya gwamman ya nada shi a matsayin Sakataren Majalisar Shura ta jihar.