
Kungiyar mahaddata alkur’ani ta kasa reshen jihar Kano ta karrama gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mukamin garkuwar mahaddata Alkur’ani na kasa.
An yi bikin karramawar ne a gidan gwamnatin jihar a ranar Talata a yayin karrama Gwarazan musabakar Alkurani ta kasa wanda aka kammala a jihar Kebbi a kwanakin baya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karramawar da ya samu tare da jan hankalin al’umar jihar Kano da a zauna lafiya a kuma ci gaba da yiwa jihar Kano addu’a domin samun zaman lafiya.

Taron karramawar ya samu halartar kwamishinan addinai Sheikh Malam Tijjani Sani Auwal da Sheikh Uba Sharada limamin masallacin Murtala da Sheikh Tijjani Bala kalarawi da sauran manyan malaman jihar Kano.